1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan ISWAP sun kashe sojojin Najeriya

Abdul-raheem Hassan
April 26, 2021

Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar dakarunta 31 a wani harin kwantan bauna da mayakan jihadi suka kaddamar kan ayarin sojojin da ke rakiyar makaman yaki zuwa wani sansani a garin Mainok a jihar Borno.

https://p.dw.com/p/3saRb
Nigeria Soldaten patrouillieren in Tungushe
Hoto: AFP/Str

Rahotanni sun ce maharan sun kwace manyan makaman soji tare da cinna wa sansanin da ke wajen birnin Maiduguri wuta. Wannan dai shi ne hari mafi muni da ya halaka sojojin Najeriya a shekarar 2021 a cewar dakarun sojin. Akalla mutane 36,000 sun mutu, kusan mutane miliyan biyu sun yi hijira sakamakon hare-haren 'yan bindiga.

Sai dai a wani sakon twitter da rundunar ta wallafa, ta ce tana bincike kan zargin ko sojojin sama ne suka kashe sojojin kasa bisa kuskure yayin bata kashi da mayakan Boko Haram a garin Mainok mai tazarar kilomita 55 daga birnin Maiduguri.