1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta ce ta kai hare hare dubu goma sha daya kan Hamas

November 1, 2023

Rikicin dai ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa sama da dubu takwas da dari biyar, mafi akasarinsu mata da kananan yara, in ji ma'aikatar lafiyar Gaza da ke karkashin ikon mayakan Hamas

https://p.dw.com/p/4YGpe
Hoto: Abed Khaled/AP/picture alliance

Isra'ila ta ce sojojinta sun kai hare hare sama da dubu goma sha daya, kan sansanonin kungiyar Hamas tun bayan da Hamas ta kai mata hari a ranar 7 ga watan Oktoba.

Karin bayaniHamas ta fitar da bidiyon mata 3 'yan Isra'ila

Rikicin dai ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa sama da dubu takwas da dari biyar, mafi akasarinsu mata da kananan yara, in ji ma'aikatar lafiyar Gaza da ke karkashin ikon mayakan Hamas.

Karin bayaniYakin Gaza ya hallaka mata da kanana yara kusan dubu shida 

Yayin da ita kuma Isra'ila ke cewa rikicin ya hallaka mutanenta dubu daya da dari hudu, yawancinsu mata da kananan yara.