1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta yanke wa daruruwan mutane hukuncin kisa

November 27, 2023

Hukumar da ke kula da kare hakkin 'dan Adam ta kasar Norway, ta fitar da kididdigar cewa Iran ta zartas da hukuncin kisa.

https://p.dw.com/p/4ZVMO
Hoto: Iranian Presidency/Zuma/picture alliance

Hukumar da ke kula da kare hakkin 'dan Adam ta kasar Norway, ta fitar da kididdigar cewa Iran ta zartas da hukuncin kisa har sau 700 a wannan shekara.

Hukumar ta sanar da hakan ne a shafin X wanda a baya aka fi sani da Twitter, duk da cewa ba ta sanar da adadin wadanda aka zartarwa da hukuncin kisan ba a shekarar da ta gabata.

Hukumar kare hakkin bil Adama ta kasar Iran ta ce akalla a kowacce shekara ana samun mutum 600 da ake yankewa hukuncin kisa, ciki har da wasu 8 da gwamnatin Tehran ta zarga da zanga-zangar kin jinin gwamnati a bara.

Hukumomin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa na zargin Iran da zartas da hukuncin kisa ga masu adawa da gwamnati da kuma tsirarrun kabilu marasa karfi.