1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar tabbaci kan batun nukiliyar Iran

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 31, 2022

Kasar Iran ta bayyana cewa tana bukatar kwakkwaran tabbaci daga Amirka, dangane da farfado da yarjejeniyar nukiliyar Tehran din da ta cimma da kaksashe shida ma su fada aji a duniya a shekara ta 2015 da ta gurgunce.

https://p.dw.com/p/4GGye
Makamashin nukiliya a Iran
Tashar makamashin nukiliyar Iran ta NatanzHoto: Alfred Yaghobzadeh/SalamPix/abaca/picture alliance

Ministan harkokin wajen Iran din Hossein Amirabdollahian ya bayyana haka a birnin Moscow na kasar Rasha, inda ya bukaci Hukumar Kula da Makamin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya IAEA da ta daina binciken da take yi a Iran da ya kira na siyasa. Bayan tsawon watanni 16 ana tattaunawa tsakanin Tehran da Amirka, a ranar takwas ga wannan wata na Agusta da muke ciki jami'in hulda kasashen ketare na kungiyar Tarayyar Turai EU Josep Borrell ya bayyana cewa EU din ta fito da sharadi na karshe da zai taimaka wajen farfadoa da yarjejeniyar ta 2015 da tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya gurgunta. An dai cimma yarjejeniyar ne tsakanin Iran da kasashen Amirka da Chaina da Faransa da Jamus da Rasha da kuma Birtaniya.