1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC za ta ladabtar da wadanda suka saci akwati

May 4, 2023

Daga cikin mutanen akwai wasu da suka tarwatsa rumfunan zabe da kuma wadanda suka sanar da sakamakon da ba shi da hujja, duk dai a kokari na sauya bukatun masu zabe.

https://p.dw.com/p/4Quv1
Shugaban hukumar zaben Najeriya Mahmood Yakubu
Shugaban hukumar zaben Najeriya Mahmood YakubuHoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

Kama daga wadanda suka tayar da zaune tsaye a rumfunan zabe ya zuwa ga 'yan bokon da ke takama da dogon turanci dai, Tarayyar Najeriya ta ga fari da kila rodi-rodi a zabukan kasar na 2023.

Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta ce tana shirin gurfanar da mutane 774 a cikin wasu shari'u 215 domin nuna girman laifukan da wadanda ake zargin suka aikata. Amma babban kalubalen da ke ga hukumar na iya kaiwa ya zuwa tabbatar da laifin zaben, cikin kasar da masu siyasar ke zaman iyaye na gida ga barayin kuri'ar.

Can a jihar Adamawa dai alal ga misali ana takkaddama a halin yanzu, a tsakanin dakataccen kwamishinan zabe na jihar Hudu Ari da yake fadin ba shi da laifin zaben da kuma jami'an tsaron da ke fadin yana da laifukan amsawa.

Abun kuma da yasa da kamar wuya mataki na hukumar zaben ya burge masu adawa wadanda ke ganin da sauran sake a cikin tsarin tafi da harkokin shari'ar a bangare na hukumar INEC din.

Jigon jam'iyyar PDP ta adawa Sanata Umar Tsauri ya ce ba su da kwarin gwiwa a kan matakin INEC din na kaiwa ya zuwa tabbatar da adalci bisa wadanda ake zargi da satar akwatun zaben.

Sashe na 145 na sabuwar dokar zabe ta kasar dai ya bai wa hukumar karfin ikon hukunta masu laifin zabe na kasar. Amma kuma babu tabbas ko hukumar ta INEC din za ta iya samar da hujjojin tabbatar da laifukan  wadanda ake zargi da aikata laifukan zaben.