1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar zabe ta kammala shirin fara zabe

Uwais Abubakar Idris
February 24, 2023

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta ce ta shirya tsaf don gudanar da zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya da za’a gudanar awannan Asabar duk fadin kasar.

https://p.dw.com/p/4NxWE
Nigeria Wahlen 2023
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Ganawa ce dai da ta tunfaye dukkanin wasu bayanan da ake son ji daga bakin hukumar zaben Najeriyar mai zaman kanta a kan wannan zabe na Najeriya, inda shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya ce duk wasu shirye-shirye da ake bukata sun kammala domin hatta kudaden da suke bukata babban bankin Najeriyar ya sama masu.

Batun rarraba kayayyakin zaben dai muhimmi ne a Najeriyar sanin yanayin kasar da wasu wuraren sai an yi amfani da jiragen ruwa da ma na sama, sannan ga matsalar da akan fusknata a zabubhukan baya na rashin isar kayayyakin zaben a kan lokaci, ko wane hali ake ciki a yanzu a game da rarraba kayan zaben?.

Dubban masu sa ido a kan zaben Najeriyar da suka fito daga kungiyoyi daban-daban na cikin kasar da ma kasashen waje ne suka saurari wannan bayani da hukumar zaben ta bayara wanda a bisa al'ada shine jawabi na karshe da ake jira kafin zaben. 

Hukumar ta ce ‘yan Najeriya sama da milyan 87 ne suka karbi katin jefa kuri'a wadanda ake sa ran za su bi sabon shugaba daga cikin ‘yan takara 18 da ke fafatawa a zaben na shugaban Najeriya da na ‘yan majalisun dokokin da kuma na datawa da wakilai.