1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kotun Turai kan sauyin yanayi

Abdullahi Tanko Bala
April 9, 2024

Alkalai a kotun tarayyar Turai sun yanke hukunci mai armashi da ya faranta wa masu rajin kare muhalli kan bukatar gwamnatoci su yi azama waje kare gurbatar muhalli.

https://p.dw.com/p/4eaRG
Greta Thunberg da Rosmarie Wydler-Walti
Greta Thunberg da Rosmarie Wydler-WaltiHoto: Christian Hartmann/REUTERS

Babbar kotun kare hakkin bil Adama ta tarayyar Turai ta yanke hukunci muhimmi na kare muhalli, kan karar da wata kungiyar mata ta shigar da ke da nufin tilasta wa gwamnatocin kasashe cika alkawuran da suka dauka na rage gurbatar hayakin masana'antu.

A daya daga cikin kararrakin uku, kotun ta amince da korafin wasu tsofaffi mata yan kasar Switzerland cewa gazawar gwamnatin wajen kula da rage hayakin masa'antu ya saba yancinsu na bil Adama.

Masu rajin kare muhalli dai sun danganta nasarorin da aka samu a baya ga hukunce hukuncen shari'a.

Wannan dai shi ne karon farko da wata kotu ta kasa da kasa ta yanke irin wannan hukunci da ya danganci sauyin yanayi.