1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Miliyoyin 'yan Najeriya na fargabar yin zabe in ji HRW

February 6, 2023

Kungiyar Human Rights Watch ta baiyana damuwa kan halin tsaron Najeriya da ke barazana ga damar 'yan kasa na yin zabe cikin kwanciyar hankali.

https://p.dw.com/p/4N94N
Yan bindiga sun hallaka mutum fiye da 60 a Katsina
Yan bindiga sun hallaka mutum fiye da 60 a KatsinaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

A wani abun da ke iya kai wa ya zuwa barazana mai girma ga makomar zaben tarrayar Najeriya, kungiyar Human Right Watch mai fafutukar kare hakki na dan adam ta ce, ana tsorata miliyoyin 'yan zabe na kasar a kokari na kai wa ya zuwa iya zaben.

A wani rahoton da ta fitar da safiyar wannan Litinin, Human Right Watch din ta ce, hadari na tada hankali yana mamaye tarrayar Najeriyar a halin yanzu, kuma yana barazana ga kokarin miliyoyi na 'yan kasar na kai wa ya zuwa babban zabe a kasar.

Human Rights Watch
Human Rights WatchHoto: John MacDougall/AFP/Getty Images

Rahoton ya ce, gaza kai wa ya zuwa hukunta masu laifin zaben 2019 da kuma tashe-tashe na hankulan da ke karuwa a sassa daban-daban cikin kasar na barazana ga masu zabe na kasar na 2023.

Mai bincike ta kungiyar a tarrayar Najeriya Aniete Ewang dai ta ce, duk da cewar hukumar zaben kasar ta INEC ta gurfanar da mutane 18 da laifin satar kuri'a da tada hankali a zaben bayan, har ya zuwa yanzu babu hukunci daga kotunan kasar bisa batun. Kuma ko bayan nan tashi na hankalin da ke ta tashi yanzu a sassan cikin kasar na haifar da fargaba a zuciyar 'yan zabe na kasar.

Barazanar tsaro a gabanin zaben Najeriya
Barazanar tsaro a gabanin zaben NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/Alamba

Wannan na janyo tsoro da tambayoyin ko 'yan kasa za su iya zaben cikin zama na lafiya? Tambayoyin ko hukumar zaben za ta iya samar da mutane da kayan zaben da ake bukata domin zaben ko kuma wadanda rikicin ya raba da muhallinsu za su samu damar iya zaben a sabbabi na wuraren da suke?

Kama daga jihar Nasarawa zuwa Katsina da ma sassa daban-daban na kudanci na kasar gwammai aka kai ga hallakawa a wani abun da ke kara fitowa da irin girman barazanar da ke iya tsallakawa har ya zuwa batun na zabe a kasar.

Hukumar zabe ta kasar INEC na takama da jerin wasu kungiyoyi na tsaro kusan 27 da ke da nauyin samar da tsaro yayin zaben.

Tarrayar Najeriyar dai na tsakanin iya kai wa ya zuwa ingantaccen zaben da ke iya burge 'yan kasar da ma bakinta, da fuskantar barazanar har ga makoma ta kasar da ke dada nuna alamun rabuwar addini da kabila.