1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon Shugaban Masar Mubarak ya rasu

Abdullahi Tanko Bala
February 25, 2020

Allah ya yiwa tsohon Shugaban kasar Masar Hosni Mubarak rasuwa yana da shekaru 91 bayan ya sha fama da jinya

https://p.dw.com/p/3YOe6
Ägypten Mubarak Aussage Prozess Mursi Muslimbrüder
Hoto: Reuters/A. A. Dalsh

Mubarak ya yi mulkin Masar na tsawon shekaru 30. An hambarar da gwamnatinsa a sakamakon zanga zangar gama gari a shekarar 2011. 

Watanni biyu bayan da ya sauka daga karagar mulki aka kama shi inda aka tsare shi a gidan yari da kuma asibitin soji har zuwa shekarar 2017 lokacin da aka sake shi bayan da kotun daukaka kara ta wanke shi daga tuhumar da aka yi masa ta bayar da umarnin kisan masu zanga zanga.

Yan Masar da dama wadanda suka zauna zamanin mulkin Mubarak sun baiyana lokacin a matsayin na kama karya da kuma jari hujja.

Gwamnatin kasar ta Masar ta baiyana zaman makoki na kwanaki uku domin nuna alhini ga mamacin.