1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tashin farashin abinci a Najeriya

April 16, 2024

Najeriya tana fuskantar hauhawar tashin farashin abinci a cikin kasar mafi tasiri a tarihi, yayin da farashin kudin Dala ke sauka inda aka sauya da kudin kasar na Naira.

https://p.dw.com/p/4erGi
Kayan abinci a Najeriya
Kayan abinci a NajeriyaHoto: Ubale Musa/DW

 

Tashin farashin kudin Dala dai aka rika ambato cikin rikicin na hauhawa ta farashin kaya a cikin Najeriya a lokaci main isa. To sai dai kuma wata kiddiga cikin kasar na cewar har yanzu hauhawar tana kara yawa duk da faduwar farashin na Dala. Wani sabon rahoton hukumar kiddidigar kasar dai tace an kalli hauhawar farashin da ta kai kaso 33 a cikin dari cikin watan Maris na jiya. A Najeriyar da yan kasar ke fatan sauki daga faduwar farashin Dala.

Karin Bayani: Najeriya ta ce yarjejeniya da Jamus ta taimaka kan samar da lantarki

Abinci kan iyakar Najeriya
Abinci kan iyakar NajeriyaHoto: KOLA SULAIMON/AFP/Getty Images

Sabuwar kiddidigar dai na kara fitowa fili da irin girman rikicin da ke gaban kasar da ke da fata game da rage farashin Dala na iya kai wa ya zuwa sauki na rayuwa tsakanin mutane. Mohammed Isyaku Tofa dai na zaman shugaban kungiyar masana'antu ta kasar reshen jihar Kano, kuma ya ce da akwai sauran aiki a tsakanin faduwar Dalar da saukin rayuwa. Batun abinci dai na zaman na kan gaba a hauhawar farashin in da a karon farko ya hau da kusan kaso 40 cikin 100 cikin watan jiya na Maris.

Tallafin gwmnatin kasar dai ya gaza tasirin rage radadin a tsakanin al'ummar da ke zaman jiran ruwa na damina a cikin barazana ta yunwa a gari. Rikicin rashin Dala ko karancin kaya dai, kimanin rumbuna 22 a cikin 33 na gwamnatin kasar dai na dauke ne da abinci na masu kasuwa.