1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin gwamnati na dab da tsayawa cak a Amirka

September 30, 2023

Harkokin gwamnati na dab da tsaya cak a Amirka sakamakon wata takkadama da ta barke a tsakanin 'yan majalisar dokokin kasar kan kudaden tafi da ayyukan gwamnati.

https://p.dw.com/p/4WzbT
Majalisar Dokokin Amirka
Hoto: Anna Moneymaker/Getty Images

'Yan jam'iyyar Republican dai sun ki aminci da yarjejeniyar wucin gadi domin ci gaba da bayar da kuudaden gudanarwar gwamnatin kasar. Ana dai ganin idan har ba a cimma matsaya ba a wannan Asabar din na ci gaba da samar da kudaden, akwai yiwuwar harkokin gwamnatin kasar su tsaya cak daga ranar Lahadi.

Takaddamar za ta shafi daruruwan ma'aikata a kasar wadanda za a tilastawa tafiya hutu ba biya, yayin da sojoji da wasu ma'aikatan da ake tsananin bukatar ayyukansu za su ci gaba da aiki ba tare da albashi ba.

Masana harkokin tattalin arziki na cewa, idan wannan barakar ta tilasta tsayar da harkoki, za ta yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasar.