1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya hallaka gwamnan Taliban

Abdullahi Tanko Bala
March 9, 2023

Wani gwamna da wasu mutane biyu sun rasa rayukansu a wani hari a Afghanistan. Babu kungiyar da ta dauki alhakin harin sai dai kasar ta sha fuskantar hare haren 'yan IS tun bayan da Taliban ta karbi mulki.

https://p.dw.com/p/4OSRI
Afghanistan | Taliban-Sicherheitspersonal
Hoto: ATIF ARYAN/AFP/Getty Images

Wani harin kunar bakin wake da aka kai ofishin gwamnan lardin Bakh a arewa maso yammacin birnin Kabul a Afghnistan ya hallaka gwamnan lardin da kuma wasu mutane biyu.

Gwamnan da aka kashe Daud Muzmal a baya ya jagoranci yaki da mayakan IS a gabashin lardin Nangarhar kafin ya zama gwamna a shekarar 2022.

'Yan IS sun tsananta kai hare hare a Afghanistan tun bayan da Taliban ta karbi ragamar mulki a 2021.

Hare haren sun shafi fararen hula da 'yan Shi'a marasa rinjaye da kuma jami'an tsaro 'yan Taliban.

Gwamna Muzmal shi ne jami'i mafi girman mukami da aka kashe tun bayan da Taliban ta dawo kan karagar mulki.