1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe Shugaba Jovene Moise na Haiti

July 9, 2021

Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani, bayan halaka shugaban kasar Haiti Jovenel Moise da wasu mutanen da ba a tantance ba kawo yanzu suka yi.

https://p.dw.com/p/3wAmF
Haitis Präsident Jovenel Moise
Marigayi shugaban kasar Haiti Jovenel Moise da aka yi wa kisan gilla a gidansaHoto: Metin Aktas/picture alliance/AA

Wasu mutane ne da suka yi wa Shugaba Jovene Moise na Haitin dirar mikiya da makamai, inda suka bindige shi tare da jikkata mai dakinsa waccce aka kai ta asibiti. Claude Josephe shi ne mukaddashin firaministan na Haiti: "Ba mu san wadanda suka aikata ta'asar ba, mutanen da suka kai hari gidansa suna magana ne da Turancin Ingilishi da kuma yaren Spain, matarsa ta samu raunuka sosai, tana bukatar samun kulawa."

Jovenel Moise wanda dan kasuwa ne da ke da kimanin shekaru 53 a duniya, an zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekara ta 2016. Ba shi dai da cikakkiyar kwarewa a kan sha'anin shugabanci, a kasar da rashin tsaro ya yi mata katutu da kuma garkuwa da mutane da kungiyoyin 'yan daba masu karbar kudin fansa ke yi. Hakan dai ya sanya ana zargin shugaban da gaza yin wani abu domin kawo karshen lamarin. A ranar Litinin din da ta gabata ne shugaban ya nada sabon firaminsta da kawo yanzu bai kama aiki ba. an nada Ariel Henry da nufin shirya zabe kafin karshen shekara ta 2021, bayan kira daga Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar Tarrayar Turai, saboda yana gudanar da mulki ne babu majalisa sai dai kudurorin doka da ake aiwatarwa.

Symbolbild Gewalt in Haiti
Rashin tsaro ya ta'azzara a Haiti, guda daga cikin kasashe mafiya talauci a duniyaHoto: Jean Mark Herve Abelard/imago images/Agencia EFE

Tun da farko an shirya gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan kundin tsarin mulkin kasar, domin kara bayar da karfin iko ga gwamnati a cikin watan Yuni da ya gabata aka dage. Tun daga lokacin da aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekara ta 2016, Moise ya nada firaminista guda  bakwai. Mukaddashin firaministan Claude Joseph ya ce suna cikin nadama: "A matsayina na firaminista, mun yi tir da wannan kisa na shugaban kasa. Ina yin kira ga al'umma da su kwantar da hankula tare da hadin gwiwar ministan cikin gida, za mu yi kokarin tabbatar da komai ya tafi daidai. Kawo yanzu, komai na cikin kulawar hukuma."

Tun a farkon watan Yuni ne ake gwabza fada tsakanin kungiyoyin 'yan daba masu gaba da juna a babban birnin kasr Port au-Prince, wanda a ciki aka kashe mutane 15. Hakan ya sa mutane na ficewa daga kasar da ke zaman guda cikin kasashe mafi talauci a duniya, wanda kuma halin da aka shiga zai iya kara dagula al'amuran tsaro a kasar.