1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadarin mota ya kashe mutane a Najeriya

November 22, 2022

Wani hadari mai muni da ya auku a yankin arewa maso gabashin Najeriya ya salwantar da gomman rayuka a wannan Talata. Hadari ne da ya hada wasu motoci biyu.

https://p.dw.com/p/4Jv0M
Hoto: Pierre Boussel/AFP/Getty Images

Kimanin mutane 37 ne hukumomi suka tabbatar da cewa sun mutu sanadiyyar wani mummunan hadarin mota da ya auku da ranar yau a tsakanin garuruwan Mainok da Jakana da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu na jihar Yobe.

Shaidu sun ce motocin safa biyu ne suka yi taho mu gama sanadiyyar fashewara tayar daya daga cikin su, sannan suka kama da wuta inda fasinjojji suka kone kurmus.

Babban jami'i na hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC a shiyyar, Rotimi Adeleye ya tabbatar wa wakilinmu Al Amin Suleiman Muhammad fauwar lamarin.