1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadarin jirgin ruwa ya kashe yara a Najeriya

May 11, 2023

Rahotanni da ke fitowa daga jihar Sokoto a Najeriya, na cewa kananan yara 15 suka nitse a ruwa yayin kuma da wasu 25 suka bata a wani hadarin jirgin ruwa da ya faru.

https://p.dw.com/p/4RBce
Hoto: AP/picture alliance

A cewar hukumomi hadarin ya faru ne lokacin da yaran ke kan hanyarsu ta komawa gida daga kauyen Dundeji bayan sun yiwo ice daga wane bangare na kogin Shagari.

Bayanai sun tabbatar da cewa jirgin da ke dauke da yaran wanda ya yi lodi fiye da kima ya nitse ne cikin kogin, inda 'yan mata 13 da kuma 'yan maza 2 suka salwanta.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai lamarin ya faru.

Ko cikin watan Afrilun bara ma dai wani hadarin jirgin na ruwa ya yi sanadiyyar kananan yara 29 a kusa da kauyen gidan Magana a dai kogin na Shagari da ke a jihar ta Sokoto.