1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar ficewar UAE daga OPEC ya karya farashin mai

Ramatu Garba Baba
March 6, 2023

Hadaddiyar Daular Larabawa ta fara nazarin ficewa daga Kungiyar OPEC a sakamakon korafin da ta jima tana yi kan iyakance mata kason man da ya kamata ta fitar.

https://p.dw.com/p/4OHxu
Kungiyar masu arzikin man fetur
Kungiyar masu arzikin man feturHoto: RYAD KRAMDI/AFP/Getty Images

Farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya samu koma baya, tun bayan da Hadaddiyar Daular Larabawa ta fara tattaunawa a game da yiwuwar ficewarta daga Kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin mai a duniya, sakamakon korafin da ta jima tana yi kan iyakance mata kaso mafi karanci da za ta dinga haka a kowa ce rana.

Tuni aka soma hasashen abin da ka iya biyo bayan wannan matakin da ka iya girgiza kungiyar tare da karya karfin tasirinta a kasuwannin mai na duniya. Tun lokacin da Hadaddiyar Daular Larabawan ta nemi shiga cikin kungiyar ta OPEC, aka shata mata sharadi kan adadin man da za ta iya hakowa, wanda ke yin nakasu ga kudaden shiga ga kasar a cewar hukumomi.