1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taiwan na fuskantar barazanar guguwa

Binta Aliyu Zurmi
September 3, 2023

Sama da jiragen sama guda 250 aka dakatar da sauka da tashinsu a babban filin jirgin sama na tsibirin Taiwan, a yayin da kasar ke dakon saukar mamakon ruwan sama gami da mahaukaciyar guguwar Haikui.

https://p.dw.com/p/4VtqZ
Taifun «Saola» - Hongkong
Hoto: Suomi Npp/Noaa-Nasa/Planet Pix via ZUMA Press Wire/dpa

Guguwar Haikui na gudun sama da kilomita 150 a kowace sa'a guda, wannan ya sa  Firaministan China Chen Chein-jen ya bukaci al'ummar da mahukuntan yankin Taiwan da su kasance a kusa da juna. Yanzu haka dai akalla mazauna 3,000 na fuskantar barazana a wani yankin da ake hasashe guguwar za ta fi yin barzana.

Tuni aka kwashe wasu mutane 290 ya zuwa sansanonin wushingadi har sai an ga wucewar guguwar, hukumar hasashen yanayi a Taiwan ta ce karfin guguwar na kara karuwa idan aka kwatanta da yadda ta fara a ranar Asabar, kuma tana tinkarar yankin kudancin kasar China daga Taiwan. Ana ganinn gudunta ka iya kaiwa har kilimita 170.