1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gomman bakin haure sun mutu a Italiya

February 26, 2023

Rahotanni daga Italiya sun yi nuni da cewa, an gano gawawwakin bakin haure kimanin 43 a gabar ruwan kudu maso gabashin kasar sakamakon kifewar da kwale-kwalensu ya yi.

https://p.dw.com/p/4NzqT
Hoto: Giuseppe Pipita/ZUMA/ANSA/IMAGO

A cikin sanarwar da masu gadin tekun suka fitar, sun ce an ceto rayukan wasu bakin haure 8. Sanarwar ta kara da cewa, kwale-kwalen na dauke da bakin haure kimanin 100 ciki har da mata da kuma jarirai, kana bakin hauren sun fito ne daga kasashen Iran da Afghanistan da kuma Pakistan.

Tuni dai aka tura da tawagar gudanar da aikin ceto da suka hada da jami'an kwana-kwana da kuma wadanda suka kware a iyo. Firanministan Italiya Giorgia Meloni ta nuna kaduwarta kan bakin hauren da suka rasa rayukansu ta na mai daura alhakin hakan kan masu safarar jama'a.

Kasashen Italiya da kuma Spaniya na ci-gaba da nuna damuwarsu kan samun adadi mafi yawa na bakin haure da ke tsallakawa Turai ta tekun Bahar rum da nufin samun ingantaciyar rayuwa.