1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Girgizar kasa a Taiwan ta hallaka mutane 4 da jikkata 60

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 3, 2024

Girgizar kasar mai karfin maki 7.2 a ma'aunin Richter, ta tada igiyar ruwan tsunami da kuma haddasa motsin kasa a wasu sannan kasar da kuma Japan

https://p.dw.com/p/4eNAZ
Hoto: CNA/AFP

Girgizar kasa a Taiwan ta hallaka mutane 4, tare da jikkata wasu guda 60 a Larabar nan, baya ga rushewar gidaje da dama, kamar yadda hukumar kashe gobarar kasar ta sanar.

Karin bayani:Girgizar kasa ta halaka mutane a Taiwan

Hukumar kula da yanayi ta kasar ta ce girgizar kasar mai karfin maki 7.2 a ma'aunin Richter, ta tada igiyar ruwan tsunami da kuma haddasa motsin kasa a wasu sannan kasar da kuma Japan.

Karin bayani:Japan: Shekaru biyar da bala'in Tsunami

An dai soke sufurin jiragen kasa a wasu manyan biranen kasar, tare da ci gaba da nazartar al'amura, bayan faruwan wannan girgizar kasa mafi muni da Taiwan ta fuskanta a cikin shekaru 25.