1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Ghana ta samu rigakafin maleriya

April 13, 2023

Masana kimiyyan sun ce wannan nasara ce da bincikensu na shekaru 30 ya samo tun bayan da suka dukufa lalubo rigakafin cutar maleriya da a duk shekara ke kashe mutum kimanin 600,000, galibi kananan yara a kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/4Pz5z
Hoto: Maxwell Suuk/DW

Hukumomin kasar Ghana sun amince a fara amfani da sabuwar allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro ko kuma maleriya a kasar. Amincewa amfani da rigakafin wacce jami'ar Oxford da ke Birtaniya ta sarrafa shi ne karo na farko da wata kasa a duniya ta yi domin kariya daga maleriya.

Jami'an da suka hada rigakafin sun ce gwajin da suka yi a kan kananan yara na kasar Burkina Faso ya nuna cewa allurar na da karfin kaso 80 cikin 100 na bayar da kariya daga kamuwa da cutar cizon sauron.

Sanarwar da jami'ar Oxford din ta fitar ta ce kawo yanzu rigakafin za ta takaita ga kananan yaran kasar Ghana da ke a tsakanin watanni 5 zuwa 36, rukunin mutanen da suka fi hatsarin mutuwa daga wannan cuta.