1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: John Mahama zai sake tsayawa takara

May 14, 2023

Babban jami'iyar adawa ta National Democratic Congress a Ghana ta zabi tsohon shugaban kasar, John Mahama a matsayin wanda zai iya mata takarar shugaban kasa a zabe na 2024.

https://p.dw.com/p/4RKkg
Afrika Ghana Präsidentschaftswahlen  John Dramani Mahama
Hoto: Nipah Dennis/AFP/Getty Images

A zaben da manbobin jam'iyyar suka kada a ranar Asabar, Mahama mai shekaru 64 ya sami nasara da kashi 98.9.

Wannan ne dai karo na uku da Mahama zai tsayawa takarar neman kujerar shugaban kasar Ghana kuma ke zuwa a na biyu bayan shugaba Nana Akufo-Addo a zabukan kasar na shekarun 2016 da 2020. Ana sa ran siyasa ta dau zafi a kasar a zabe mai zuwa yayin da kasar ke fuskantar durkushewar tattalin arzki wanda ya haifar da tsadar rayuwa da kuma bore a kasar.

A shekarar 2012 ne dai shugaba Mahama a lokacin yana mataimakin shugaban kasa ya dare kan madafun ikon Ghana, wanda ya maye gurbin tsohon shugaba John Atta Mills da ya mutu. Har kawo yanzu dai jam'iyya mai mulki a kasar bata zabi wanda zai mata takarar shugaban kasar ba.