1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Shirin tsagaita wuta na watanni biyu a Gaza

Abdourahamane Hassane
January 23, 2024

Wani rahoton da wata kafar yada labarai ta Amirka ta bayyana ya nuna cewar gwamnatin Isra'ila na shirin tsagaita bude wuta na tsawon watanni biyu a yakin da take da Hamas.

https://p.dw.com/p/4bajF
Hoto: ISRAEL DEFENSE FORCES/REUTERS

 An mika tayin ga masu shiga tsakani daga Masar da Qatar, in ji tashar labarai ta Axios Abin da zai ba da damar sako dukkanin mutanen da aka yi garkuwa da su, da har yanzu Hamas ke rike da su a zirin Gaza. Sannan a labarin da jaridar Wall Street Journal ta kasar Amurka ta fitar, ta ce kasashen Larabawa ma suna aiki kan shawarar samar da kasashe biyu bayan kawo karshen yakin. A saboda haka, Saudiyya ta yi tayin amincewa da Isra'ila a matsayin mayar da martani ga kafa kasar Falasdinu.