1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

G20 ta amince da samar da kasar Falasdinu

February 23, 2024

Ministocin harkokin wajen kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 sun nuna goyon baya ga samar da kasashe biyu daura da juna tsakanin Isra'ila da Falasdinu a yankin Gabas ta Tsakiya domin samun masalaha ta dindindin.

https://p.dw.com/p/4cmaL
Wakilan kasashen G20 a birnin  Rio de Janeiro na Brazil
Wakilan kasashen G20 a birnin Rio de Janeiro na Brazil Hoto: Ricardo Moraes/REUTERS

Shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 sun cimma matsayar samar da 'yantacciyar kasar Falasdinu da za su zauna daura da juna da Isra'ila a matsayin masalaha ga rikicin da aka shafe shekaru da dama ana fama da shi a Gabas ta Tsakiya, a taron kungiyar da Lula da Silva ya jagoranta tare da gabatar da mukala a madadin shugabannin kan bukatar hakan.

Taron na kasashe G20 da ke gudana a birnin Rio de Janairo na kasar Brazil na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dokokin Isra'ila ta kada kuri'ar amincewa da bukatar Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na yin fatali da duk wata bukata ta samar da kasar Falasdinu.

Tun bayan da Isra'ila ka kaddamar hare-haren kan mai uwa da wabi a zirin Gaza, wannan ne karon farko da akasarin shugabannin G20 suka amince da kuduri guda na bukatar kafa kasashe biyu masu 'yanci, a cewar guda daga cikin jami'an diflomasiyyar Brazil Mauro Vieira.