1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brazil ta ce ba za ta kama Putin idan ya je kasar ba

September 10, 2023

Duk da babu wanda ya yi yunkurin kama shi bayan umurnin kotun ICC, shugaban na Rasha ya ci gaba da kauce wa halartar manyan taruka na duniya, inda ya kan tura ministansa na harkokin waje domin ya wakilce shi.

https://p.dw.com/p/4WAPi
Hoto: Alexander Zemlianichenko/AP/dpa/picture alliance

Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula ya ce babu wanda zai kama shugaba Vladimir Putin na Rasha idan har ya halarci taron shekara mai zuwa na kungiyar G20 ta kasashe masu karfin tattalin arziki da zai gudana birnin Rio de Janeiro na Brazil.

A yayin wata hira da aka yi da shi a wajen taron kwanaki biyu na G20 da ya gudana a kasar Indiya, shugaban na Brazil ya ce za su gayyaci Shugaba Putin a taron kungiyar na badi, yana mai cewa shi da kanshi zai halarci taron kungiyar BRICS da za a yi a Rasha domin nuna wa Shugaba Putin cewa babu wani abu boyayye a zuciyar mutanen Brazil.

A watan Maris din da ya gabata ne dai kotun hukunta masu aikata muggan laifuka ta duniya, ICC, ta bayar da sammacin a kamo mata Shugaba Putin bisa zargin sa da aikata mummunar ta'asar yaki a Ukraine.