1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fifa ta dakatar da shugaban kwallon kafar Spain

Binta Aliyu Zurmi
August 26, 2023

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta dakatar da Luis Rubiales mai shekaru 46 daga shugabantar hukumar kwallon kafa ta kasar Spain kan sumbatar wata 'yar wasa.

https://p.dw.com/p/4Vc1l
FIFA Fußball Frauen-WM | Luis Rubiales küsst Jennifer Hermoso
Hoto: Noe Llamas/Sport Press Photo/ZUMA Press/picture alliance

Biyo bayan sumbatar yar wasa Jenni Hermoso a lebenta bayan da Spain ta doke Ingila a wasan karshe na Kofin Duniya wanda ya janyo ce-ce-ku-ce mai zafi.

Ko baya ga dakatar da shi daga shugabantar hukumar kwallon kafa a kasar Spain, kazalika FIFA ta haramtawa Rubiales daga shiga harkokin wasa a kasar ta Spain da ma a matakin duniya baki daya.

Duk da kiraye-kirayen da aka dinga yi a ciki da wajen kasar na ya sauka daga mukaminsa kafin matakin na FIFA na yau, Mista Rubiales ya ki yin murabus.