1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MNSD Nassara ta soki lamirin shirin zabe a Nijar

Salissou Boukari AMA
December 3, 2019

A Jamhuriyar Nijar jam’iyyar MNSD Nassara da ke gungun kawancen masu mulki ta soki lamirin yadda ake gudanar da kidayar masu zabe na zamani a kasar, inda ta ce ta gano tarin kura-kurai.

https://p.dw.com/p/3UA4r
Wahlplakat für Seini Oumarou Niger
Hoto: DW/M.Kanta

A ranar 15 ga watan Octoban da ya gabata ne aka soma kidayar masu zabe a Jamhuriyar Nijar, bayan dan tsaiko da aka fuskanta sakamakon wata tangarda na’urar kidayar. Sai dai tun da aka soma wannan kidaya bangarori dabam-daban sun jima suna zargin ‘yan wata jam’iyya da laifin kwaso mutane daga ko’ina ba bisa ka’ida ba domin sanya su a cikin kidaya ta kafafen sadarwa na zamani, sai gashi ita ma jam’iyyar MNSD Nassara da ke bangaran masu mulki ta fito karara ta hanyar aikewa da wata wasika ga hukumar zabe mai zaman kanta ta CENI, inda ta ce ta lura ba’ayin wannan kidaya cikin yadda dokokin kasa suka tanada, inda ta yi kira da maza a dauki matakan dakatar da wannan tabargaza.

Jam’iyyar MNSD Nassara na daga cikin jiga-jigan jam'iyyun ‘yan adawa a baya, amma daga bisani ta canza sheka ta koma bangaran masu mulki inda aka kirkirowa shugabanta Alhaji Seini Oumarou wata kujera ta musamman ta mukamin wakilin shugaban kasa na musamman. Sai dai duk da haka jam’iyyar na shirin tsayawa takara a zaben shugabancin kasa, kana kuma ta fara fitowa fili tana fallasa abubuwan da take gani za su iya zama cikas wajen cikar burinta na zabe a nan gaba.

Bangarori dabam-daban musamman ma ‘yan kungiyoyin fararan hulla na yi wa matakin da MNSD Nasara ta dauka da wata manufa, a daidai lokacin da ita kuwa hukumar zabe mai zaman kanta CENI ba ta fito fili ta yi karin haske kan korafe-korafen jam'iyyar ba.