1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan takara 20 za su fafata a zaben Laberiya

Evelyn Kpadeh Muntaqa Ahiwa
October 9, 2023

Hukumar zaben kasar Laberiya ta yi alkawarin samar da zabe mai tsafta kuma wanda zai karbu ga kowa. Sai dai kuma a gefe guda bangarorin adawa na shakku kan yiwuwar samun abin da hukumar ta zabe ke fadi a Laberiyar.

https://p.dw.com/p/4XIsE
George Weah shugaba mai barin gado na Laberiya
George Weah shugaba mai barin gado na LaberiyaHoto: dpa

Wannan ne karon farko da Laberiya ke shirya zabe da kanta, tun bayan janye sojojin Majalisar Dinkin Duniya a kasar da ke yankin yammacin Afirka. Shugaba mai ci George Weah na daga cikin wadanda ke takara, inda ake da 'yan takara 20 da za su fafata a zaben shugaban kasa. Ana dai kallon tsohon mataimakin shugaban Laberiyar Joseph Boakai a matsayin babban mai kalubalantar Shugaba George Weah na jami'yyar CDC. Akwai kuma mata biyu da ke cikin jerin masu takarar. Akalla akwai ‘yan Laberiya miliyan biyuda hukumar zaben kasar ta yi wa rajista, kuma wasun su sun bayyana abin da suke fata  daga wanda zai mulki kasar na tsawon shekaru shida nan gaba:Jimmy Frank  wani malamin makaranta da ke cewa,  "tattalin arzikin kasarmu na ja baya. Idan har akwai yadda za a samu sauyin gwamnati, ina ganin abu na farko da zai dace a fifita shi ne bincike kan barayin gwamnati da suka rusa arzikin. Dole mu san yadda suka tafiyar da gwamnatin kasarmu cikin shekaru shida da suka wuce. Sai bukatar maida hankali kan gina hanyoyi domin samun damar fitar da amfanin gona - da nake ganin zai rage nauyin arzikin da muke fama da shi din nan.”

Yamutsi ya yi sanadin mutuwar mutane uku a Labariyar cikin harkokin zaben

Krankenhaus in Monrovia ECOMIL Soldat
Hoto: AP

Tun bayan kaddamar da yakin neman zabe ne dai ake ta ganin wasu ‘yan fitintinu masu  nasaba da zaben daga masu goyon bayan ‘yan takara, abin da tuni ya haddasa mutuwar mutum uku. Wannan ne ma ya sanya wasu ‘yan Laberiyar ke kiran da a bi a sannu domin samun zaben cikin kwanciyar hankali. "A yanzu zabe mai adalci muke so, don sam ba ma son rifgima a wannan kasa. Ga matasa, galibinsu ba su ga yaki ba, don haka mu dai ba mu son fada a ko'ina a kasarmu. Matasan su amince da sakamako kawai a ci gaba. Wanda ya ji ba a yi masa daidai ba ya tafi kotu ko kuma ya jawo hankalin kasashen duniya. Wannan kuma Caroline ce da ke fadin "Fatana zabe ya kasance cikin kwanciyar hankali. ‘Ya'yanmu su samu ilimi. Mu mun ga yaki a baya mun kuma san abin da muka sha. Mun dandana wahalar yaki.” Masu sharhi kan siyasar kasar dai na cewa abu ne mai wuya, a iya sanin wanda zai lashe zaben shugaban Laberiyar inda ake ganin kowace jam'iyya ta fafata sosai a yakin neman kuri'u sannan su ma masu zabe na cike da zumudi kan ‘yan takarar. Kasashen duniya dai sun cesuna sa ido kan yadda za ta kaya a zaben na Laberiya.