1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawaye sun hana zaman lafiya a Goma

Abdourahamane Hassane RGB
March 4, 2023

Yan tawayen M23 na kokarin tunkarar Goma bayan kwace iko da garin Mushaki, wanda ke da nisan kasa da kilomita talatin daga garin Goma.

https://p.dw.com/p/4OEFG
Rundunar sojin Kwango
Rundunar sojin KwangoHoto: Dai Kurokawa/dpa/picture alliance

A gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, 'yan tawayen M23 na kokarin tunkarar Goma. Garin Mushaki, wanda ke da nisan kasa da kilomita talatin daga Goma, ya fada hannunsu, kafin sojojin Kwango su karbeshi. Amma ana ci gaba da gwabza fada da mayakan M23 a kan tsaunukan wannan yanki mai tuddai. Yanzu haka ana aza ayar tambaya a game da inda 'yan tawayen ke samun kudaden sayen makamai har suka sha karfin dakarun gwamnatin.

Da farko dai yankunan da ke karkashin ikon kungiyar masu dauke da makamai na da tarin arzikin ma'adinai, bugu da kari, karbar haraji ba bisa ka'ida ba daga jama'a, al'ada ce da kungiyoyin 'yan tawaye suke yi domin samun kudaden shiga

Masu adawa da sojojin kasar Ruwanda
Masu adawa da sojojin kasar RuwandaHoto: Aubin Mukoni/AFP

Kwararru masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya a kan kasar,  sun bayyana alal misali, a cikin wani rahoto da aka gabatar a watan Disamba na 2022 ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewar, harajin da Kungiyar M23 ta karba daga jama'a a kan iyakokin Bunagana da Kitagoma ya taimaka wajen samar da kudaden ayyukan kungiyar. Hakazalika a cewar Majalisar Dinkin Duniya, kungiyar na karbar kusan dala dubu 27,000 a kowane wata a kan iyakar ta Bunagana kadai.

Wadanda rikici ya raba da gidajensu a Kwango
Wadanda rikici ya raba da gidajensu a KwangoHoto: Guerchom Ndebo/AFP/Getty Images

Kungiyar ta M23 na yin shelar cewa 'yan gudun hijira 'yan kabilar Tutsi 'yan asilin Ruwanda da ke zaune a arewacin Kwagon, suma suna taimaka mata. Akwai dimbin al'ummar Tutsi na Kwango da ke zaune a Ruwanda, mutanen da suka dade suna can kuma ba za su iya komawa gidajensu ba a Kwango. Sojojin Kwango na zargin Ruwanda da jibge sojoji a gabashin Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Kwangon 356 domin karfafa 'yan tawayen M23 abin da ya sa dangantaka tsakanin kasahen biyu ta yi tsami.