1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta kama hanyar kakaba wa Nijar takunkumin karya arziki

Mouhamadou Awal Balarabe
October 23, 2023

Ministocin harkokin wajen Tarayyar Turai sun amince da wani tsari da zai ba ta damar kakaba takunkumi kan gwamnatin da ta hau kan kujerar mulkin Nijar ta hanyar hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum a karshen watan Yuli.

https://p.dw.com/p/4XuSG
 Annalena Baerbock ta Jamus na daga cikin wadanda suka halarci taron Luxemburg
 Annalena Baerbock ta Jamus na daga cikin wadanda suka halarci taron LuxemburgHoto: Thomas Koehler/photothek/IMAGO

A cikin wata sanarwa ga manema labarai bayan taro da ministocin harkokin wajen EU suka gudana a Luxembourg, ofishin kantoman harkokin wajen Turai ya ce tsarin na doka zai bada damar kakaba takunkumi ga mutane da hukumomin da ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaro a Nijar.  Har ila yau, wadanda ke da hannu a duk wani yunkuri da ya yi karar tsaye ga kundin tsarin mulki da tafarkin dimokuradiyya za su kasance a sahun wadanda EU za ta ladabtar.

Karin bayani: Matsalolin tsaro bayan juyin mulki a Nijar

 Irin wannan takunkumi ya tanadi karbe kadarori da hana samun tallafin kudi daga Turai da kuma haramta wa jami'ai shiga yankin naTurai. Dama dai mambobi 27 na EU sun  yi Allah wadai da karbe mulki da sojoji suka yi, lamarin da ya sa kungiyar tarayyar Turai dakatar da tallafin kudi da take bai wa Nijar tare da dakatar da duk wani hadin gwiwa a fannin tsaro.

Karin bayani: Tiani ya gode wa 'yan Nijar da suka ba da tallafi

Nijar na fuskantar tsauraran takunkuman karya tattalin arziki daga kungiyar ECOWAS/CEDEAO tun a karshen watan Yuli. Ita dai kasar ta yankin sahel da ke fama da matsalar tsaro ta tilasta wa Faransa janye sojojinta 1,400 da ta girke a kasar. .