1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta ce kawuna sun rabu a Rasha kan yakin Ukraine

Suleiman Babayo M. Ahiwa
June 26, 2023

Ministocin harkokin wajen kasashen Tarayyar Turai sun ce boren da Rasha ta gani a karshen mako ya fito da rarrabuwa a tsakanin masu rike da ikon kasar kan yakin Ukraine.

https://p.dw.com/p/4T5RY
Babban jami'i a kungiyar EU, Josep Borrell
Babban jami'i a kungiyar EU, Josep BorrellHoto: Frederick Florin/AFP via Getty Images

Lokacin taron ministocin sun amince da taimakon kimanin kudi Euro milyan dubu-uku da rabi ga Ukraine bisa taimakon soja da bayar da horo. Ministocin harkokin wajen daga kasashe 27 mambobin kungiyar kasashen ta Tarayyar Turai sun gana a kasar Luxembourg bayan abin da ya faru a karshen mako inda Yevgeny Prigozhin shugaban kamfanin sojojin haya na Wagner ya kwace iko da shelkwatar sojojin Rasha da ke kudancin kasar tare da maci zuwa birnin Moscow kafin kulla yarjejeniyar da ta janyo ya yi watsi da matakin da ya dauka, inda ya umarci mayakansa su koma gabashin Ukraine. Catherine Colonna ministar harkokin wajen kasra Faransa ta ce akwai tambayoyi masu yawa kan abin da ya faru a karshen mako a kasra ta Rasha kuma kasashen Turai suna ci gaba da saka ido kan halin da ake ciki.

Belgien EU-Verteidigungsaußenminister
Hoto: Geert Vanden Wijngaert/AP Photo/picture alliance

Babban jami'in kula da harkokin wajen kungiyar kasashen Tarayyar Turai, Josep Borell ya ce Shugaba Vladimir Putin yana ganin irin sakamakon abin da ya yi kan kirkiro mayakan na Wagner da shugabanta Yevgeny Prigozhin, kuma abin da ya faru a kasar ta Rasha ya nuna tasirin ci gaba da taimakon kasar Ukraine domin ta tsaya da kafafunta duk da kutsen da take ci gaba da fuskanta daga Rasha. Josep Borell na mai cewa:

"Ina tsammani wannan yana da himmancin kan mu ci gaba da taimakon kasar Ukraine. Saboda abin da ya faru a karshen mako ya nuna karara akwai rarrabuwa kan yakin Ukraine a tsakanin masu rike da madafun ikon Rasha inda yanayin ya shafi harkokin tafiyar da siyasar kasar. Muna bin abin da ke faruwa, amma yanzu za mu ci gaba da taimakon Ukraine fiye da kowane lokaci a kan abin da za mu iya."

Ita ma Annalena Baerbock ministar harkokin wajen Jamus ta ce Shugaba Vladimir Putin na Rasha yana kassara kasarsa da kansa saboda yakin da ya kaddamar a kan kasar Ukraine.