1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Gidauniyar taimakon jinkai a Siriya

Abdullahi Tanko Bala
June 15, 2023

Kungiyar tarayyar Turai ta kaddamar da gidauniyar kasa da kasa don taimaka wa ayyukan jinkai ga miliyoyin 'yan Siriya da yaki ya tagaiyara tun shekarar 2011.

https://p.dw.com/p/4Scon
Josep Borrell I EU sagt weitere Hilfe für Ukraine zu
Hoto: Zheng Huansong/Xinua/IMAGO

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da yake jawabi a taron ya bukaci kasashe masu hannu da shuni su taimaka don ceto rayuwar al'ummar Siriya daga halin kuncin rayuwa da suka sami kansu a ciki.

"Ya ce roko na mai sauki ne, ku taimaka mana mu taimaki al'ummar Siriya, muna bukatar dala biliyan daya da miliyan dari daya, wannan ita ce gidauniyar tallafi mafi girma da muka kaddamar kuma ba mu da lokaci da za mu jinkirta."

Wannan shi ne taro na bakwai da hedikwatar tarayyar Turai a Brussels ke gudanarwa domin tallafa wa game da makomar Siriya da yankin baki daya, kuma karo na farko tun bayan da Siriya ta dawo cikin kungiyar kasashen larabawa bayan girgizar kasar da ta yi mummunan ta'adi a kasar a farkon wannan shekarar.

Kungiyar tarayyar Turai ta yi alkawarin bada gudunmawar euro miliyan 560 kwatankwacin dala miliyan 600

A shekarar da ta gabata taron ya tara dala biliyar 6.7. A yanzu Majalisar Dinnkin Duniya na fatan kungiyar tarayyar Turai da kasashe mambobinta da ke zama a kan gaba wajen bada gudunmawar jinkai ga Siriya da kuma yankin za su kara yin hobasa.