1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daina hawa motoci masu amfani da fetur

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 14, 2023

Majalisar Tarayyar Turai, ta amince da haramta sayar da motocin da ke fitar da gurbataccen hayaki masu amfani da man fetur da kuma diesel na da shekara ta 2035.

https://p.dw.com/p/4NT6z
Motoci l Fetur | EU | Tarayyar Turai
Daina sayar da motoci masu amfani da fetur a TuraiHoto: Michael Sohn/AP/picture alliance

Wannan mataki na majalisar Tarayyar Turai dai, ya nunar da cewa, abin da ya rage shi ne sanya hannu kan wannan kudiri ya kuma zama doka. Koda yake wannan mataki na fuskantar turjiya daga bangaren masu ra'ayin 'yan mazan jiya da ke da rinjaye a majalisar, kudirin ya samu amincewa daga mambobi 340 yayin da 279 suka nuna kin amincewa kana 21 suka yi rowar kuri'unsu.