1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Uwais Abubakar Idris
April 19, 2024

Gwamnatin Najeriya ta yi shellar neman tsohon gwamnan jihar Kogi Yahya Bello da ya tsere a kokarin kama shi da hukumar EFCC ta yi don fuskantar zargin cin hanci na sama da Naira bilyan 80

https://p.dw.com/p/4ezmD
Hoto: Africa Studio - Fotolia.com

Wannan dambarwar da ke faruwa tsakanin tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriyar zagon kasa ta EFCC inda lamarin ya zama abin kunya saboda yadda suke wasan buya domin Yahaya Bello da ya arce ta amfani da gwamnan jihar da ya bashi kariya ta ficewa da shi a motarsa ya harzuka gwamnatin Najeriyar saboda gujewa fuskantar tuhuma ta zargin da ake yi masa. 

Ministan shari'a na Najeriya ya yi gargadi ga duk kokarin kawo cikas ga aikin hukumar EFCC, yayin da sufeto janar na 'yan sandan Najeriya ya janye daukacin ‘yan sandan da ke bai wa tsohon gwamnan kariya, ita ma hukumar kula da shige da fice ta sanya sunansa a jerin wadanda ake nema, don haka an hana shi tafiya ta duk wata tashar jiragen saman Najeriyar. 

A yayinda da ba'a san inda tsohon gwamnan ya boye ba, hukumar EFCC ta bayyana cewa duk inda yake za ta kamo shi don fuskantar shari'a, kuma in ta kama ta nemi taimakon sojoji ne za ta yi haka. Wannan ya sanya tambayoyi mabambanta a kan hatsarin da ke tattare da ci gaba da sanya sojojin Najeriya a harkar da ta shafi hukumomi na farar hula irin na ‘yan sanda da jami'an tsaro na farin kaya na DSS

A baya dai hukumar ta EFCC ta yi irin wannan samamen da zagaye gidan tsohon gwamman jihar Imo Rochas Okorocha a ranar 22 ga watan Mayun 2022 inda ta samu nasarar cafke shi, amma a wannan karon akasin haka aka samu. Masana harakar shari'a na bayyana cewa tserewa fuskantar shari'a ba mafita bace a ko ina a duniya kuma abin kunya ne ga kasa, domin wata rana zai fada komar EFCC