1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dusar kankara ta gurgunta harkoki a Jamus

Abdullahi Tanko Bala
January 17, 2024

Zubar dusar kankara mai yawa ta janyo tsaiko a yankuna da dama a kudanci da yammacin Jamus wanda ya sa manyan filayen jiragen sama na kasar dakatar da tashin daruruwan jirage.

https://p.dw.com/p/4bNcu
Dusar kankara ta hana tashin jirage a Frankfurt da Munich a Jamus
Dusar kankara ta hana tashin jirage a Frankfurt da Munich a JamusHoto: Matthias Balk/dpa/picture alliance

Filin jirgin saman Frankfurt ya soke tashin jirage 570 a wannan Laraba saboda tsananin zubar dusar kankarar da kuma santsi musamman a yammaci da kudancin Jamus.

A filin jirgin saman Munich a jihar Bavaria an soke tashin jiragen sama 254, fiye da kashi daya cikin kaso uku na jiragen da aka tsara za su tashi a safiyar wannan rana.

A Saarbrücken kuwa da ke yammacin Jamus mai iyaka da kasar Faransa an dakatar da dukkan harkoki saboda yawan zubar dusar kankarar.