1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arzikin Jamus na tangal-tangal

Ahmed Salisu LMJ
April 8, 2020

Rahoton shekara-shekara da ake fitarwa kan tattalin arzikin Tarayyar Jamus ya nuna cewar tattalin arzikin kasar zai samu koma baya da kusan kaso 10 cikin 100 sakamakon annobar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3aeCf
Coronavirus | Deutschland | Schutzmaske
Hoto: Reuters/M. Tantussi

Rahoton wanda cibiyar nan ta IFO da wasu takwarorinta da ke sanya idanu kan tattalin arzikin Jamus suka saba fidda shi a karshen lokacin sanyin hunturu, ya nuna cewar tattalin arzikin kasar a rubu'i na biyu na wannan shekarar zai samu koma baya da sama da kaso tara cikin 100, kuma a cewarsu hakan na da nasaba da bullar annobar COVID-19 wadda ta sanya da dama daga cikin kamfanoni da hukumomi da ma'aikatu a Jamus din, suka takaita ayyukan nasu ko ma dakatar da su baki daya, a wani mataki na daklile bazuwar cutar ta COVID-19 da ta zama ruwan dare gama duniya. Wannan yanayi da tattalin arzikin ke shirin shiga inji rahoton shi ne mafi muni da za a gani tun bayan da IFO din ta fara fidda rahoto kan tattalin arzikin kasar a cikin shekarar 1970.
Minsitan kudin kasar Peter Altmaier ya ce kasar za ta fuskanci durkushewar tattalin arzikinta bayan da ya shafe shekaru 10 yana bunkasa, to amma a ganinsa lamura fa za su iya sauyawa idan aka dauki wasu matakai wadanda suka hada da janye dokar da hukumomi suka sanya ta takaita zirga-zirga da gudanar da ayyuka a masana'antu da ma'aikatun kasar. 

Berlin Finanzminister Olaf Scholz
Ministan kudin Jamus Peter AltmaierHoto: picture-alliance/AA/A. Hosbas

Masassarar tattalin arziki

Duk da cewar ministan kudin Jamus din na ganin warware wannan matsala ta samun koma bayan tattalin arzikin kasar ka iya kasancewa mai sauki, a bangare guda masana tattalin arziki na cewar abin fa ya wuce yadda ake tunani. Farfesa Rolf Langhammer na cibiyar nan ta Institute for World Economy da ke cikin jerin wadan suka fidda wannan rahoton, na ganin lamarin fa na wannan jikon ya sha banban da irin wanda aka gani a baya.

Yayin da Farfesa Rolf Langhammer ke nuni da irin jan aikin da ake da shi a gaba na dawo da tattalin arzikin kasar kan diga-digansa, tuni hukumomin Berlin suka fara daukar matakai na ganin sun yi wa wannan matsala dabaibayi, inda suka fidda tsabar kudi da yawansu ya kai triliyan guda na Euro domin tallafawa kamfanoni da ma'aikatu da ma 'yan kasuwa da suka fara ji a jika. 

Deutschland Professor Rolf J. Langhammer
Masanin tattalin arziki Rolf LanghammerHoto: picture-alliance/ dpa

Matakan ceto tattalin arziki

Wannan mataki da gwamnatin kasar ta dauka ya sanya wasu daga cikin masana tattalin arziki a kasar irinsu Timo Wollmershaeuser hasashen ficewar kasar daga wannan kangi na koma bayan tattalin arziki cikin kankanin lokaci, musamman ma idan aka yi la'akari da irin yadda ya samu bunkasa da ma girkuwa a tsukin shekaru 10 da suka gabata. Tuni ma dai Mr. Wollmershaeuser ya yi hasashen cewar a shekara mai kamawa, tattalin arzikin Jamus din zai iya farfadowa da sama da kaso biyar cikin 100.