1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Cin-hanci

Somaliya ta shahara a batun cin-hanci

February 16, 2023

Wasu kasashen Afirka na ci gaba da kaurin suna a fannin cin-hanci da karbar rashawa ko sama da fadi da dukiyar kasa, inda Somaliya da Sudan ta Kudu suka kasance a matsayin farko.

https://p.dw.com/p/4NbRM
Transparency International | Cin-hanci | Afirka
Transparency International ta ce cin hanci ya yi kamari a Somaliya da SudanHoto: Soeren Stache/picture alliance/dpa

Wannan dai na kunshe ne cikin rahoton da kungiyar Transparency International mai yaki da cin-hanci ta bayyana, inda ta ce matsalar na ci gaba da kamari a Kamaru duk da daure dimbin ministoci da aka yi kan laifin sama da fadi da dukiyar kasa. Somliya dai ta ciri tuta a fannin matsalar cin-hanci da karbar rashawa, baya da yakin basasa da ya daidaita kasar. Ko da Transparency International sai da ta sanya ta sahun farko, yayin da Sudan ta kudu ke bi mata baya. Ba wai kasashen da ke fama da yake-yake a Afirka ne kadai suka yi kaurin suna a fannin cin-hanci ko sama da fadi da dukiyar kasa ba, daidai da kasashe da ke da kwarya-kwaryan zaman lafiya da wadata na cikin wannan rukuni. Najeriya da Equatorial Guinea da Burundi da Zimbabwe da Yuganda da Laberiya da kuma Kamaru, na daga cikin kasashen da wannan matsala ta yiwa katutu. Sai dai duk da ikirarin fadi tashin da gwamnatocin kasashen ke yi na ganin sun yi yaki da matsalar cin hanci da rashawa, har kawo yanzu hakarsu ta gaza cimma ruwa. 

Kamaru l Tsaro | Matsala | Cin-hanci
Rashin tsaro na zaman guda daga cikin matsalolin KamaruHoto: DW/D. Köpp

A baya-bayan nan ma kotu ta yanke wa tsohon ministan tsaron Kamaru Edgar Alain Mebe Ngo'o hukuncin shekaru 30 a gidan yari, bayan da ta same shi da laifin sama da fadi da kimanin dala miliyan 40 na kudin haraji a lokacin da yake kan aiki. To sai dai har yanzu, kasar ta Kamaru na fama da wannan matsala. 'Yan jarida da dama ne aka daure yayin da aka kashe wasu a kan ayyukansu, musamman ma wadanda suka mayar da hankali wajen binciken a kan matsalolin da ke da nasaba da cin-hanci.Samson Wedse da ke bibiyar al'amuran da suke shafi cin-hanci a birnin Yaounde na Kamaru, ya shaidawa tashar DW cewa rayuwarsu na cikin hadari mussaman 'yan jarida da suke bincike kan laifuka da suka shafi cin-hancin da rashawa. Ga Nancy Suwaibo da ke fafutukar yaki da cin-hanci da rashawa a Kamaru,a halin yanzu dukkanin bangarorin kasar na fama da wannan matsala, domin haka akwai buktar a gudanar da tarukan wayar da kan jama'a tun daga tushe wajen yaki da wannan dabi'a. A makwannin da suka gabata hukumar da yaki da cin-hanci da rashawa ta Kamaru ta ce za ta gudanar da gamgamin wayar da kan jama'a tun daga makarantun firamare har zuwa jami'a, a wani mataki na yaki da cin-hanci da rashawar.