1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Pakistan za ta smau rance

Suleiman Babayo AMA
July 5, 2023

Gwamnatin Firaminista Shehbaz Sharif ta Pakistan ta bayyana yuwuwar samuin matsaya kan samun rance daga hukumomin kudi na duniya.

https://p.dw.com/p/4TS6P
Pakistan I Firaminista Shehbaz Sharif
Firaminista Shehbaz Sharif na PakistanHoto: Fabrice Coffrini/AFP

Gwamnatin Pakistan ta bayyana fata kan cewa asusun ba da lamuni na duniya, IMF, zai amince da tsarin karban rance da kasar take bukata ranar 12 ga wannan wata na Yuli zuwa mako mai zuwa ke nan.

Firaminista Shehbaz Sharif da ke jagorancin kasar da ke yankin kudancin nahiyar Asiya ya tabbatar da haka.

Karkashin tsarin kasar ta Pakistan tana bukatar kimanin kudi Dalar Amirka milyan dubu-uku na gajeran lokaci domin zaburar da tattalin arzikin kasar. Bangarorin biyu sun kwashe kimanin watanni takwas suna tattaunawa kafin cimma wannan matsaya da yanzu duk suka saka hannu a kai.