1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO na ingiza mambobinta zuwa yaki

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 12, 2023

China ta zargi kungiyar Tsaro ta NATO da yin tunani irin wanda ta yi a lokacin yakin cacar-baka, bayan da mahalarta taron NATO din a birnin Vilnius suka yi suka ga Beijing.

https://p.dw.com/p/4TmR6
NATO | Taro | Ukraine | Rasha | Chaina
Chaina ta nazrgi NATO da yin kalamai ma su nasaba da yakin cacar-bakaHoto: Aytac Unal/AA/picture alliance

Kakakin ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta China ya nunar da cewa, kungiyar Tsaron ta NATO ta gaza tantance abin da yake daidai da kuma wanda ba daidai ba. Ya kara da cewa kungiyar na daukar wasu matakan da ba su dace ba, wanda kuma tuni China ta sa kafa ta yi fatali da su. A cewarsa duk da NATO ta yi ikirarin cewa ita mai bayar da kariya ce, amma tana zuga mambobinta su yi ta kashe kudi a fanonin sojansu da  fadada karfin ikonsu a kan iyakoki. Kana ya yi zargin NATO din da ingiza mambobin nata, su je takalar fada ko fito na fito a yankin Asia da Pacific.