1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China da Amirka sun daidaita kan sauyin yanayi

Abdullahi Tanko Bala
November 11, 2021

A kokarin hada kai don yaki da sauyin yanayi, Amirka da Chaina sun cimma sabon kudiri.

https://p.dw.com/p/42tOr
John Kerry beim COP26
Hoto: Alastair Grant/AP/picture alliance

Chaina da Amirka sun jaddada kudirin su na hada hannu tare da yin aiki da dukkan bangariri domin karfafa aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris.

Bangarorin biyu sun amince za su kafa kwamitin aiki da cikawa domin cimma kudirin kare muhallin kamar yadda jakadan musamman na Chaina Xie Zhenhuwa ya shaidawa taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi da ke gudana a Glasgow na yankin Scotland 

"Yace Chaina da Amirka suna da abubuwa da dama da suka hada kawunansu fiye da abubuwa da suka raba su ta fannin sauyin yanayi, kuma bangarorin biyu na da kudiri mai karfi na shawo kan matsalolin muhalli. Muna fata wannan kudiri zai taimaka a cimma nasarara da ake bukata."

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya yaba wa yarjejeniyar Chaina da Amirka yana mai cewa muhimmin matakin cigaba ne.