1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

CAF: za a bayyana kasar da zata dauki nauyin wasanni a cikin wannan mako

November 12, 2014

Kasar Moroko ce dai ta jawo wannan sauyi bayan da kin amincewa ta karbi bakuncin saboda tsoran kada a shigar mata da cutar Ebola me saurin kisa.

https://p.dw.com/p/1DlyF
Marokkanische Fußballnationalmannschaft
Hoto: AFP/Getty Images/F. Senna

Za a bayyana sabuwar kasar da za ta dauki nauyin gasar wasannin kwallon kafar nahiyar Afrika ne nan da kwanaki uku bayan da kasar Moroko ta bayyana kin daukar nauyin gasar saboda tsoron Ebola kamar yadda hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Afirka, CAF, ta bayyana a wannan Laraba.

Shugaban hukumar ta CAF Issa Hayatou ya ce za su tattauna da kasashen da ke da muradin karbar bakuncin gasar wasannin, Se dai da ya ke bayani ga manema labarai ya ce za a iya fiskantar tsaiko a lokacin da za a gudanar da wasan saboda wannan sauyi.

Hayatu ya ce wannan mataki zai bata ran masu daukar nauyin wasannin dama wadanda suka shiga shirin gudanar da wasannin inda kowa ke ganin laifin hukumar ta CAF kuma wannan shi ne abin da hukumar ta yi ta gaya wa kasar ta Maroko.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo