1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Burundi mai barin gado ya mutu

Zulaiha Abubakar
June 9, 2020

Gwamnatin kasar Burundi ta sanar da mutuwar shugaban kasar sakamakon ciwon zuciya a wannan Talatar bayan ya yi fama da gajeriyar jinya.

https://p.dw.com/p/3dXbU
Burundi Wahlkampf Präsident Pierre Nkurunziza
Hoto: AFP

Sanarwar ta kara da cewar a lokacin rayuwarsa marigayi Nkurunziza ya yi imani da cewar Ubangiji ya zabe shi ne musamman domin ya shugabanci kasar ta Burundi, Nkurunziza ya shiga harkokin mulki a shekara ta 2005 bayan da zauren majalisar dokokin kasar ya zabe shi. Daga baya bukatar sake mulkin kasar a wa'adi na uku ta jefa kasar a rikicin siyasar da ya haifar da asarar rayukan farar hula akalla 1,200 yayin da daruruwan al'umma suka rasa muhallansu bayan hukumomi sun kaddamar da kamen masu adawa da kuma matsantawa kafafen yada labarai lamba.

Mutuwar shugaban kasar ta Burundi mai barin mulki ta zo a lokacin da kotu ta tabbatar da nasarar Evariste Ndayishimiye a matsayin sabon shugaban kasar, yanzu haka dai fadar mulkin kasar ta kebe mako guda domin juyayin mutuwarsa tun daga wannan Talatar.