1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burkina Faso ta kori Jakadun Faransa

April 18, 2024

Burkina Faso ta kori wasu ma'aikatan diflomassiyar Faransa uku bisa zargin shirya makarkashiyar kifar da gwamnati kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito

https://p.dw.com/p/4evy4
Ibrahim Traore shugaban kasar Burkina Faso
Ibrahim Traore shugaban kasar Burkina FasoHoto: Kilaye Bationo/AP/picture alliance

Wannan dai wata alama ce da ke nuna ci gaba da tsamin dangantaka tsakanin Burkina Fason da kuma uwar gijiyarta Faransa.

A cikin wata sanarwa da Burkina Faso ta aike wa ofishin jakadancin Faransa a ranar Talata, ta bukaci mutanen uku su fice daga kasar cikin sa'o'i 48.

Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta ce mutanen su ne  Gwenaelle Habouzit, Herve Fournier da kuma Guillaume Reisacher.

Ofishin harkokin wajen Faransa dai bai ce uffan ba a kan wannan batun kawo yanzu.

Tun bayan da ya karbe madafun iko ta hanyar juyin mulki a watan Satumban 2022, shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar Captain Ibrahim Traore ya ci gaba da nesanta kasarsa da Faransa wacce ta mulki Burkina Fason tun a shekarar 1960.