1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Halitta da Muhalli

Bunkasar al'umma na barazana ga lafiya a Kano

Nasir Salisu Zango ZUD/MA
July 11, 2023

Cunkoson mutane na barazana ga mutanen jihar Kano, inda masana ke nuna yadda lamarin ke haddasa matsalar numfashi daidai lokacin da jama’a ke kauce wa tsarin kayyade iyali.

https://p.dw.com/p/4Tj9w
Kano | Cunkoson jama'a wajen zaben shugaban kasa
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Yawan mutane a jihar Kano na kawo cunkoso da turnukewar yanayi wanda masana lafiya da muhalli ke cewar babbar barazana ce ga zamantakewar al’umma. Dubban kananan yara ne a kusan kowacce rana ke yawo a kan manyan titunan Kano a cikin hayakin ababen hawa da masana ke cewa na hadassa dumamar yanayi. Wannan na daya daga cikin abubuwan da suka fi damun masu fafutukar kare muhalli a daidai lokacin da a wannan Talata ake bikin Ranar Yawan Al’umma ta Duniya.

Bunkasar al’umma a jihar Kano dai a cewar masana na neman zama ‘’taron yuyu’’ a wasu lokutan idan aka yi la’akari da yadda wasu iyayen ke haifar ‘ya’yan suna watsi da su, lamarin da ke tilasta wa yaran yin gararamba a gari babu cikakkiyar tarbiya. Duk hakan dai na faruwa ne daidai lokacin da gurbatar yanayi a dalilin yawan al’umma ke kawo matsalolin yanayi wanda a lokuta da dama ke haddasa barkewar cututtukan numfashi da amai da gudawa. Unguwanni da dama a birnin Kano cike suke da kananan gidaje wanda suke cike da mutanen da zaman gidajen ke zame musu matsala har ta kai numfashi ya gurbata.

Kano | Jerin a daidaita a layin sayen man fetir
Yawan baburan a daidaita sahu na daga cikin ababan hawa da ke fitar da hayaki mai gurbata muhalli a KanoHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Abubakar Ibrahim magidanci a Kano ya kuma shaida wa DW takaicinsa bisa yadda yawancin mutane ke da al’adar sakin jiki ana haihuwa barkatai cikin kuntataccen yanayi. Ya bukaci jama’ar jihar musamman wanda ba su da muhalli mai kyau da su takaita haihuwa.

Hukumomin lafiya a jihar ta Kano na nuna damuwa a kan barazanar da yawan al’umma ke yi wa lafiyar jama’ar jihar. Malam Abdullahi Ismail Kwalwa, darakta a ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ya bayyana cewar rashin tsari wajen karuwar jama’a a Kano ya fara kawo wa jihar tarin matsaloli musamman ma kalubale ta fuskar lafiya.

‘’Matukar al’umma za ta rika karuwa ba tare da daukar matakai ba, to yawan zai iya zama taron yuyu’’ in ji Dr Murtala Uba, malami a Jami’ar Bayero.