1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Borno: Hari ya halaka mutane da dama

June 10, 2020

Masu aikin jin kai da ceto na ci gaba da neman mutane da ba a ji duriyarsu ba, sanadiyyar mummunan harin da mayakan Boko Haram su ka kai a jihar Borno da ke Najeriya, yayin da adadin wadanda suka mutu ke karuwa.

https://p.dw.com/p/3da7q
Mutmaßlicher Boko-Haram-Angriff in Nigeria
Hare-haren Boko Haram na ci gaba da halaka mutane a NajeriyaHoto: picture-alliance/AP/Jossy Ola

Karamar hukumar ta Gubio dai na da nisan kilomita 96 daga Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno. Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutane sama da 65, bayan da aka samu kartin gawarwarki a kan 59 da tun farko aka ruwaito sun mutu a harin da ke zaman mafi muni a baya-bayan nan.

Gudun tsira da rai

Ana dai ci gaba da nemo mutane da ake fargabar sun gudu da harbin bindiga a jikinsu. Wannan hari dai ana ganin kamar na ramuwar gayya ne, kasancewar mayakan na Boko Haram sun yi zargin mutanen kauyukan na bayar da bayanai na sirri ga jami'an tsaro a kansu.

Niger Symbolbild Armee
Sojoji na ikirarin nasaraHoto: AFP/S. Ag Anar

Yanzu haka dai kusan kowa ya tsere daga wannan kauye da mafi yawan mazaunansa manoma da makiyaya ne da su ka dogara da kungiyar 'yan sintirin da su ka kafa, da ke ba su kariyar tsaro daga 'yan bindiga da ke kai hare-hare da kuma sace musu abinci da dabbobi. Mayakan na Boko Haram dai na zafafa hare-haren da suke kai wa a wannan lokaci, abin da ya sa mazauna wannan yankin ke kukan cewa hannun agogo ya koma baya a harkokin tsaro. Rundunar sojojin Najeriyar dai na cewa jami'anta na bakin kokarinsu, kuma a kullum suna samun gagarumar nasara a wannan yaki da suka ce sun ma karya lagon mayakan.

Muhimmancin farautar mahara

Sai dai al'umma na ganin dole sojojin su sauya salon yaki ta hanyar kai hari ga mayakan a duk inda suke, duk da cewa wasu jami'an tsaro na cewa babu su ba a kuma san inda su ke ba. A ta bakin Sanata Ali Ndume shugaban kwamitin da ke kula da ayyukan sojojin a majalisar dattawa ta Najeriyar dai, ko wadanda ba jami'an tsaro ba sun san inda mayakan na Boko Haram suke. Babu shakka wannan hari zai bude sabon shafi na zargin da ake yi wa jami'an tsaro musamman sojoji, na kasa magance hare-haren, duk da sababbin kayan aiki da kuma makudan kudi da ake kashewa domin kawo karshe wannan rikici.