1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iyakar Jamus da Birtaniya za ta kasance a rufe

Abdoulaye Mamane Amadou
December 20, 2020

Jamus za ta rufe iyakokinta na sama ga kasashen Biratniya da Afirka ta Kudu biyo bayan bullar wani nau'in annobar COVID-19 mai saurin yaduwa tsakanin al'umma.

https://p.dw.com/p/3myc7
Coronavirus London | Letzter Zug nach Paris | Reisende warten
Matafiya a Birtaniya, na cikin fargabar sake rufe iyakokin Turai saboda sabuwar corona.Hoto: Stefan Rousseau/PA Wire/dpa/picture-alliance

Majiya daga ma'aikatar lafiyar Jamus na cewa, yanzu haka hukumomin kasar na ci gaba da tattauna batun rufe iyakar da Birtaniya ta sama da ta jiragen kasa, duba da fargabar da ake fuskanta na yaduwar sabuwar cutar ga jama'a.

Idan har Jamus din ta kai ga daukar wannan mataki, hakan na nufin ta bi sahun kasar Holland wacce ita ma a yau Lahadi ta bayyana rufe kofofinta na sama ga kasar ta Biraniya wacce ke fuskantar bullar sabuwar kwayar cutar ta COVID-19 sabon samfuri, wanda kawo yanzu likitoci suka kasa kai ga ganowa.

Tuni ita ma kasar Beljiyam ta bayar da sanarwar rufe iyakokinta da Birtaniya ta sama da ta jiragen kasa tun daga yau Lahadi har tsawon kwanaki biyu kamar yadda wani kusa a gwamnatin ya sanar.

Ko a ranar Asabar din da tagabata dai, firministan Birtaniyan Boris Jonhson ya ce sabon nau'in kwayar cutar da ya mamayi Landan, na da saurin yaduwa fiye da wanda aka sani a baya da kaso kimanin 70 cikin dari