1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: Nasara kan sojojin NAZI na Jamus

Abdullahi Tanko Bala LMJ
May 9, 2023

A birnin Moscow na kasar Rasha an gudanar da faretin sojoji domin murnar cika shekaru 78 da nasarar da Tarayyar Soviet ta samu a kan sojojin Nazi na Jamus, a lokacin yakin duniya na biyu tsakanin 1941 zuwa 1945.

https://p.dw.com/p/4R6dI
Rasha | Fareti | Nassara | Tarayyar Soviet | NAZI | Jamus
Faretin sojojin Rasha kan nasarar Tarayyar Soviet a kan sjojin NAZI na JamusHoto: Alexander Zemlianichenko/AP

Ana dai gudanar da wannan bikin a ranakun tara ga watan Mayu na kowace shekara, kuma faretin na bana a cewar ma'aikatar tsaron Rasha ya kunshi sojoji dubu 10 da suka hadar da sojoji 530 da ke fafata yaki a Ukraine. A yayin faretin tunawa da nasarar da aka yi a kan sojojin NAZI da aka gudanar a dandalin Red Square a birnin Veliky Vovgorod na Rashan, an baje kolin tankokin yaki samfurin T-34 da motar yaki samfurin komai da ruwanka Tiger da makaman kakkabo jiragen sama S-400 da makamai masu linzami samfurin Yars da kuma motoci da ke dauke da makamai masu guba. Sojoji 1,000 da suka yi shiga ta kayan sarki na zamanin yakin duniya na biyu, sun rika yi maci suna wucewa gaban shugaban kasar da manyan baki.

Karin Bayani: Gorbachev ya taka rawa wajen sauya siyasar duniya

Sai dai ba kamar shekarun baya ba, a bana an takaita bikin sannan babu shawagin jiragen yaki. Tsohon shugaban kasar Tarayyar Soviet Josef Stalin shi ne ya fara bayar da umarnin gudanar da bikin a watan Yunin 1945, inda shugaban Rasha da aka zaba ta dimukuradiyya Boris Yeltsin a 1995 ya mayar da ranar murnar nasarar da suka samu a kan sojojin Nazi na Jamus ta zama biki da za a rika yi duk shekara. A karkashin Shugaba Vladmir Putin kuma, aka mayar da ranar ta nuna karfin tasiri na makaman soji. Sai dai an soke bikin faretin a wasu garuruwa da biranen Rasha da ke iyaka da kasar Ukraine, saboda matsaloli na tsaro.

A jawabinsa shugaban Rasha Vladimir Putin da ke zaune a tsakiyar wasu tsofaffin shugabannin kasashen tsohuwar Tarayyar Soviet, ya nemi nuna karfin tasirin Rasha ta fuskar makamai. Putin ya ci alwashin sai sun sami nasara a kan Ukraine yana mai cewa: "Kasashen yammacin duniya har yanzu suna nuna sun fi kowa, suna gwara kan mutane da raba tsakanin al'umomi da tunzura zubar da jini da juyin mulki da kuma dasa kiyayya a zukatan al'umma da kuma nuna kyamar Rasha. Girman kansu da shisshigi sun haifar da bala'i, wannan shi ne dalilin masifar da mutanen Ukraine suke fuskanta a yanzu kuma sojojinmu za su yi nasara."

Karin Bayani: Turai na tunawa da gama yakin duniya na biyu

Jawabin na Putin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kamfanin sojin haya na Rasha Wagner ya zargi sojojin Rashan da guduwa daga filin daga a Bakhmut, inda ake tsakiyar barin wuta a Ukraine. Wagner sun shafe watanni suna jagorantar fafatawa a Bakhmut, yankin masana'antu da ke gabashin Ukraine da yakin ya daidaita. Sojojin Rasha ba su tabuka wani abin a zo a gani ba, yayin yakin da suka gwabza a lokacin sanyin hunturu. A hannu guda kuma shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta tashi daga Poland zuwa Kiev, inda ta  gana da shugaban Ukraine a kokarin kasarsa na shiga kungiyar ta Tarayyar Turai. A nasa bangaren shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya sanar da cewa daga yanzuu kasarsa za ta rika yin bikin wannan rana a matsayin ranar nasara ga Tarayyar Turai. Ya kuma bukaci kungiyar ta EU ta hanzarta shigar da kasarsa cikinta.