1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin Easter a halin cutar coronavirus

Abdullahi Tanko Bala
April 10, 2020

Yayin da kasashen duniya ke cigaba da yaki da annobar cutar coronavirus shugabanni addinin addinin Kirista sun bukaci mabiyansu su gudanar da bukukuwan Easter na bana a cikin gidajensu domin kare yaduwar cutar

https://p.dw.com/p/3ajw7
Vatikan Papst Franziskus Palmsonntag
Hoto: Reuters/A. Pizzoli

Kiristoci a fadin duniya sun fara bukukuwan ibada na mako guda tare da tunawa da irin wahalhalu da mutuwa da kuma tashin Yesu Al-Masihu. Yahudawa sun fara bikin na Passover ne tun a ranar Laraba inda suke tunawa da kaurar jama'a daga Masar da kuma samun yanci daga kangin bauta.

A cikin makonni biyu masu zuwa ne kuma al'ummar Musulmi suke shirin fara azumin watan Ramadan. Mabiya addinan uku na musulmi da Kiristoci da kuma Yahudawa, jigon abubuwan da zasu gudanar yayin ibadar shine hadin kai a tsakanin al'ummomi da cin abincin dare tare ga Kiristoci ko kuma baki daki ga musulmi.

A Israila Yahudawa masu bin addinin gargajiya sun ki bin umarnin gwamnati na takaita zirga zirga yayin da kasar Saudiyya ke nazarin soke aikin hajjin bana saboda annobar corona. Yayin da wasu mabiya ke ganin lamarin da matukar wahala, ya nuna irin kalubalen da addinan ke fuskanta yayin da suka ci karo da zamani.

A waje guda dai babban limamin Yahudawa ya yi kira ga dukkan yahudawa a duniya su yi biyayya ga ka'idojin da kasashe suka bayar na takaita zirga zirga saboda cutar corona.