1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Biden ya caccaki Isra'ila kan salon yakinta a Gaza

April 10, 2024

Shugaba Joe Biden na Amurka ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Benjamin Netanyahu kan solon yakin da take a Gaza tare da yin kira da a tsagaita wuta.

https://p.dw.com/p/4ebNo
Biden ya caccaki Isra'ila kan salon yakinta a Gaza
Biden ya caccaki Isra'ila kan salon yakinta a GazaHoto: Gil Cohen Magen/Xinhua News Agency/picture alliance

Shugaba Biden ya yi wannan furici ne a daidai lokacin da kotun kolin Isra'ila ta gayyaci gwamnatin Netanyahu a wannan Laraba domin ta wanke kanta daga zargin da ake yi mata na dakile shigar da kayan agaji a yankin na Falasdinu da ya fara fama da bala'in yunwa.

A hirar da ya yi da wani gidan talabijin, Mista Biden ya ce bukatarsa daya da gwamnatin Isra'ila ita ce ta tsagaita wuta na tsawon makonni takwas ko kuma shida tare da ba da damar isar da kayan abinci da magunguna ga yankin na Falasdinu.

Sai dai a daren Talata wayewar Laraba, Isra'lar ta yi ruwan bama-bamai tare da kisan Falasdinawa a arewaci da kuma tsakiyar Gaza, a daidai lokacin da al'umma Musulmi ke bukukuwan karamar Sallah ta Eid El Fitr.

A daya gefe kuma duk da gargadin da manyan kasashe ke yi masa, mista Netenyahu ya kekesa kai da kasa kan matakin afkawa Rafah da ya bayyana a matsayin tungar karshe ta mayakan Hamas da ya sha alwashi kakkabawa.

Sai dai amma sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce yana da shakku kan cewa Israila za ta kai hari Rafah gabanin sabuwar tattaunawa a birnin Washington.