1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gini ya ruguje da mutane a Kamaru

Abdoulaye Mamane Amadou Abdouurahmane Hassane
July 23, 2023

Jami'an agaji na can na kokarin bincike ko akwai ragowar mutane a karkashin baraguzan ginin wani bene da ya rufta da jama'a arewacin birnin Douala na Kamaru

https://p.dw.com/p/4UI6K
Nachtaufnahme in Douala Kamerun
Faduwar rana a Birnin Douala, cibiyar kasuwancin kasar KamaruHoto: Thomas Imo/photothek/IMAGO

Akalla mutane 12 ne suka game da ajalinsu wasu biyar kuma suka jikkata, sakamakon ruftawar wani bene mai hawa hudu a wata unguwar da ke arewacin birnin Douala cibiyar kasuwancin kasar Kamaru.

Wani kansila na karamar hukumar ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da cewar a dare Asabar zuwa Lahadi wannan ginin ya ruguje a arewacin birnin na Douala.

Ma'aikatan agaji na ci gaba da neman wadanda suke binne a baraguzan ginin.