1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karo na shida Bayern Munich ta lashe kofin Champions lig

Mouhamadou Awal Balarabe AMA
August 24, 2020

A karo na shida kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta lashe kofin da ake wa lakabi "Kofi mai kunnuwa" inda ta zama zakarun Turai, bayan ta yi nasara kan PSG ta kasar Faransa a wasan karshe na Champions League.

https://p.dw.com/p/3hQ7U
Champions League Finale 2020 Paris vs Bayern München | Sieger Bayern München
Yan wasan Bayern rike da kofi suna murnan lashe gasarHoto: AFP/M. Childs

Wannan nasarar ta bai wa kungiyar kudancin Jamus damar zama giwa a gida, giwa a dawa, kamar a shekara ta 2013 ta zama gwarzon kwallon Jamus, sannan ta kuma lashe kofin kalubale tare da kammala kaka da kofin da aka fi kauna baya ga kofin duniya. Godiya ta tabbata ga Kingsley Coman, dan gari da Bayern Munich ta ci gari da shi, tun da shi ne ya zura daya-daya kwallon a ragar kungiyar PSG da ta raine shi kuma ta sayar da sh ga Munich. Sai dai tauraron ya sa kafa ya shure kwatanta shi da marubuta labarin wasanni ke yi da Arjen Robben ko Franck Ribéry, tsoffin 'yan Bayern da suka daga darajarta.

Fußball Champions League Finale PSG - Bayern München
PSG na jimamin kasa samun nasaraHoto: picture-alliance/dpa/Michael Regan/Getty Images via UEFA

Sai dai PSG tana ci gaba da cizon yatsa saboda gaza cika burinta na lashe kofin zakarun Turai cikin tarihinta, a daidai lokacin da ta cika shekaru 50 da kafuwa. Sau daya ne cikin tarihin kwallon kafar Faransa wata kungiya ta taba lashe kofin zakarun Turai a 1993 wacce ba wata ba ce illa Olympic de Marsaille abokiyar gabar PSG. Amma kuma wannan rashin nasara bai hana Thomas Tuchel, mai horar da 'yan wasan na babban birnin Faransa nuna gamsuwa da kamun ludayin 'yan wasansa ba, saboda wannan shi ne karon farko da suka haye zagayen dub da kusa da na karshe.

"Na fada wa kungiyar gaba daya cewa ina matukar alfahari, A kullun yana kasance abin takaici idan ka kai wannan matsayi, kuma ka kasa taka rawar gani. Amma na yi rashin kofin ne, a wasan da ya hada kungiyoyin biyu da suka cancanci kasancewa a wasan karshe."

Frankreich Ausschreitungen in Paris nach dem Champions League Finale
Magoya bayan PSG sun yi bore a ParisHoto: picture-alliance/AP Photo/M. Euler

Sai dai bayan rashin samun nasara a gasar zakarun na Turai, wasu magoya bayan PSG sun tada zaune tsaye a tsakiyar birnin Paris, lamarin da ya sa 'yan sanda kama mutane 140 musamman a kusa da Tour Eiffel ko Eiffel Tour.

Paris Saint Germain da kuma Bayern munich suna daga cikin kungiyoyin kwallon kafar Turai masu dimbin magoya baya a nahiyar Afirka ciki har da tarayyar Najeriya, inda masu sha'awar kwallon ba su yi mamakin nasarar da kungiyar Bayern din ta samu ba, idan aka yi la'akari da nasaorrin da ta samu a baya, da kuma salon wasanta.

Matan Paris Saint Germain suna ci gaba da jan zarensu.To a yayin da rukunin maza na PSG ya kasa kai bante sa a zakarun Turai, su kuwa 'yan matan Paris Saint Germain suna ci gaba da jan zarensu a wannan gasa, inda a ranar Asabar suka doke takwarorinsu na Arsenal da ci 2-1 a wasan dab da kusa da na karshe wato qauter final na champions lig ranar Asabar. Kamar dai a rukunin maza, 'yan matan PSG su kasance na biyu da za su wakilci Faransa a wasan kusa da na karshe baya ga Lyon wacce ta doke 'yan matan Bayern munich da 2-1. Sai dai a wannan karon 'yar gida za a yi domin 'yan matan PSG da Lyon za su kara da junansu don samun tikiti zuwa wassn karshe a ranar Laraba, yayin da 'yan matan Wolfsburg na jamus ke karawa da barcelona a wannan Litinin 24.08.20. 

Frauenfußball | Frisuren
Matan PSG na jan zarensuHoto: Getty Images/AFP/J. Soriano

A gasar cin karamin kofin Turai na Europa League kuwa, Sevilla FC ta Spain ce ta kai labari a ranar Jumma'a da maraice inda ta lashe Kofinta na shida cikin shekaru 14 bayan da tun 2006 bayan da ta doke Inter Milan ta Italiya da 3-2. Wannan nasarar dai na da mahimmanci ga Sevilla FC, saboda kasar su ta Spain ta kasance daya daga cikin wadannan annobar corona ta fi salwantar da rayuka, inda yawancin magoya bayan kulob din, musamman tsofaffi suka rigamu gidan gaskiya.

Tsugune ta kasa karewa hukumar kwallon kafar Cote d'ivoireA kasar Cote d'Ivoire tsugune ta kasa karewa a shirin da ake yi na gudanar da zaben sabo shugaban hukumar Kwallon kafar wannan kasa. Idan za a iya tunawa dai hukumar kwallon kafar da ake yi wa lakabi da FIF ta dakatar da kwamitin da zai shirya zabe tare da rusa tsarin zaben da aka amince da shi biyo bayan takaddamar takarar tson dan wasan kasar Dider Drogba. Sai dai cikin wata doguwar wasika da ta aika wa Cote d'Ivoire, Hukumar Kwallon Kafa ta duniya FIFA ta ce tsarin zaben bai russu ba domin shugabannin FIF ba su sanar da matsayin na su ga 'yan takara a lokacin da doka ta kayyade ba. Wannan yana nufin cewa kwamitin kula da sahihancin zaben sabon shugaban hukumar kwallon kafar kasar zai koma bakin aiki ba tare da bata lokaci ba. Tuni dai Didier Drogba tsohon keftin din les elephants ta Cote d' ivoire ya yi fatan ganin an amince da takardarsa ta takara a zaben shugaban FIF da zai gudana a ranar biyar ga watan Satumba mai zuwa.

Frankreich Paris | Ehemaliger Fußballspieler | Didier Drogba
Didier Drogba na kasar Cote d'ivoireHoto: Getty Images/AFP/F. Fife